Ibrahim Ali Amin (Little), ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa haɗakar jam’iyyun siyasa

0
15

Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP a Kano, Ibrahim Ali Amin (Little), ya fice daga jam’iyyar saboda rikice-rikicen shugabanci da rashin dimokuraɗiyya a cikin gida

Ɗaya daga cikin fitattun mambobin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) a Jihar Kano, Ibrahim Ali Amin wanda aka fi sani da Little, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar, yana mai bayyana dalilinsa da rikicin shugabanci da kuma tabarbarewar tsarin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.

A cikin wata wasika da ya aika wa Shugaban Ƙaramar Gundumar Tudun Wada da ke ƙaramar hukumar Nassarawa, little, ya bayyana cewa ficewarsa ta fara aiki nan take.

“Ina so in sanar da ku a hukumance cewa na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar PDP daga yau,” in ji wasikar.

Little, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar, ya nuna takaici kan yadda jam’iyyar ke tafiya a halin yanzu, yana mai cewa ba zata kara zama dunkulalliyar jam’iyyar ta siyasa ba.

A ƙarshe, ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa haɗakar jam’iyyun siyasa  da ke ƙoƙarin sake gina ƙasa da dawo da ainihin dimokuraɗiyya.

“Na yanke shawarar barin PDP domin shiga wannan haɗaka da ke da nufin ceton ƙasarmu da kuma dawo da sahihin tsarin dimokuraɗiyya,” ya ƙara da cewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here