An kwantar da Buhari a ICU a asibitin ƙasar Birtaniya– Rahoto

0
48

Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, na fama da rashin lafiya a kasar Birtaniya, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa an kwantar da shi a dakin kula da marasa lafiya masu tsananin bukatar kulawa (ICU) a wani asibiti da ke Landan.

Jaridar TheCable ta ruwaito daga Empowered Newswire cewa wani makusancin Buhari ya bayyana cewa ya kamu da rashin lafiya ne yayin da ya ke a Landan domin duba lafiyarsa.

Rahoton ya bayyana cewa an kwantar da shi a ICU, sai dai daga bisani aka sallame shi daga dakin kulawar makon da ya gabata, kuma yanzu haka yana samun sauƙi.

Ko da yake ba a bayyana irin cutar da ke damunsa ba, majiyoyi sun ce ana ci gaba da kula da lafiyarsa, kuma ana sa ran zai dawo gida Najeriya da zarar ya warke gaba ɗaya.

Bugu da ƙari, rahoton ya ce Mamman Daura – kawun Buhari, shima yana fama da rashin lafiya a Landan, sai dai rahotanni sun nuna cewa yana samun sauƙi.

Tsohon shugaban bai halarci bikin cika shekaru 50 da kafuwar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ba, wanda aka gudanar a Legas ranar 28 ga Mayu.

A wata wasika da ya aike wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Buhari ya bayyana cewa dalilin rashin halartar taron ya samo asali ne daga tafiyarsa ta duba lafiya zuwa Birtaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here