Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa ta kammala dawo da dukkan alhazan da suka gudanar da Aikin Hajjin bana daga kasar Saudiyya zuwa Najeriya cikin nasara.
A wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa jirgin ƙarshe mai ɗauke da alhazai 88 daga jihohin Kaduna da Katsina ya tashi daga birnin Jiddah da misalin karfe 10:30 na safe.
NAHCON ta ce wannan jirgi ya kawo ƙarshen aikin dawo da alhazan da ya ɗauki kwanaki 20, tun daga ranar 13 ga watan Yuni.
A cikin saƙon bankwana da ya isar wa alhazan, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya gode wa Allah bisa nasarar kammala aikin cikin salama da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci alhazan da su ci gaba da yi wa Najeriya addu’a domin samun sauƙin matsalolin da ke addabar ta.
Farfesa Abdullahi ya tunatar da alhazan cewa Aikin Hajji ibada ce da ke koyar da zaman lafiya da hadin kai. Ya buƙaci su ci gaba da kiyaye zumuncin da suka gina da juna a lokacin ibadar.