Ƴan gwangwan ne suka shigo da Bama-Bamai cikin Kano—Gwamnatin Kano

0
31
Abba Gida Gida
Abba Gida Gida

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci masu sana’ar sayar da kayayyakin gwangwan da su dakatar da shigo da irin wadannan kaya daga yankin Arewa maso Gabas na kasar nan zuwa cikin Kano.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Kano, AVM Ibrahim Umaru (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

A cewar kwamishinan, wannan mataki na dakatar da shigo da kayayyakin gwangwan daga arewa maso gabas, ya biyo bayan fashe-fashen bama-bamai da aka samu a jihar a kwanakin baya, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 5, da jikkata wasu da dama.

Ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa bama-baman da suka tashi a jihar an shigo da su ne cikin kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas, yankin da ya dade yana fama da rikicin Boko Haram.

Kwamishinan ya kara da cewa wannan umarni na gwamnati zai taimaka wajen kare lafiyar al’umma da hana shigowar kayan da ke barazana ga tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here