Ɓarayi ne a cikin haɗakar jam’iyyun da zasu yaƙi Tinubu—Sowore

0
32

Omoyele Sowore, ɗan gwagwarmayar kare haƙkin ɗan Adam kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, ya ce ba zai taɓa shiga haɗakar jam’iyyun adawa da ke shirin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027 ba.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Sowore ya bayyana cewa ba zai iya yin kawance da wasu ’yan siyasa da ya zarga da lalata Najeriya ba, yana mai caccakar su da laifin cin hanci da rashawa, cin amanar ƙasa da zalunci.

“Ban taɓa haɗin kai da Bola Ahmed Tinubu wajen rarraba hodar iblis a Chicago ba,” in ji shi.

“Ban shiga cikin badakalar Atiku Abubakar da ake zargin ya wawure dukiyar Hukumar Kwastam ba. Haka kuma ban taɓa zama cikin kudin da David Mark ya sata ba, waɗanda aka ware don gyaran hanyoyin sadarwa, sannan ya murƙushe burin dimokuraɗiyya a ranar 12 ga Yuni ba.”

Sowore ya zargi wasu fitattun ’yan siyasa ciki har da tsofaffin ministoci, gwamnoni da ’yan takarar shugabancin ƙasa da cewa su ne suka jefa Najeriya cikin halin da take ciki a yau.

Ya ce yana da akida mai tsauri, kuma ba siyasa ce za ta sa ya sassauta ra’ayinsa ba.

Daga karshe yace ba zai haɗa kai da ɓarayi domin yaƙar ɓarayi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here