Tinubu zai mayar da Fubara kan kujerar gwamnan jihar Rivers

0
1

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, na shirye-shiryen mayar da Siminalaya Fubara, kan kujerar gwamnan jihar Rivers, tare da yan majalisar dokokin jihar bayan dakatar dasu a watannin baya. Wannan yunkuri ya biyo bayan samun daidaito da yin sulhu tsakanin Fubara da ministan Abuja Nyesom Wike, wanda shugaban kasar ya shiga tsakanin su.

:::Gwamnatin Bauchi zata kirkiro sabbin masarautu

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyanawa jaridar Punch, cewa Tinubu, na duba yiwuwar mayar da Fubara kan kujerar sa ta gwamna bayan ganawar da suka yi a daren Alhamis a fadar shugaban kasa. Majiyar tace a cikin wannan wata na Yuli ake sa ran Fubara zai koma kan mukamin sa.

Taron ya samu halartar Fubara, Wike da kakakin majalisar dokokin Rivers da aka dakatar Martin Amaewhule.

Idan za’a iya tunawa a ranar 18 ga watan Maris ne shugaban kasa Tinubu, ya zartar da dokar ta baci a jihar Rivers, inda ya dakatar da gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da yan majalisar dokokin jihar, tsawon watanni 6, biyo bayan rikicin siyasar dake neman zama tashin hankali tare da sanya Ibok Ibas, a matsayin gwamnan riko na watanni 6.

LEAVE A REPLY

Logged in as Ismail Ishaq-Ibrahim. Log out?

Please enter your comment!