Sojoji Sun Kashe Mayaƙan Boko Haram/ISWAP Takwas a Borno

0
39
Sojoji
Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kashe aƙalla mayaƙan Boko Haram da ISWAP guda takwas, a wani artabu da ya ɓarke da yammacin Litinin a ƙauyen Manawaji, cikin ƙaramar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.

Sanarwar da rundunar Operation Hadin Kai ta fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, ranar 30 ga Yuni, 2025.

An bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon haɗin gwiwar dakarun soji da ‘yan sintirin CJTF da kuma rundunar tsaro ta Hybrid Forces, inda suka fatattaki ‘yan ta’addan a yayin faɗa mai zafi.

A cewar sanarwar, dakarun sun kashe mayaƙa takwas yayin da sauran suka tsere da raunuka. Haka zalika, an ƙwato bindigogi da harsasai daga hannun ‘yan ta’addan da aka kashe da kuma waɗanda suka gudu.

“Babu asarar rai ko raunata daga bangaren sojojin mu da sauran abokan haɗin gwiwa,” in ji sanarwar.

Hukumomin tsaro sun ce tuni aka ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin Gamboru Ngala da kewaye, domin hana mayakan sake samun kafa a yankin.

A halin yanzu dai, an tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankin, duk da cewa ana ci gaba da sanya ido don gujewa duk wata barazana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here