Matatar Dangote ta rage farashin man fetur

0
15
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur daga naira 880 zuwa naira 840 ga dillalan da ke siyan man daga matatar, a wani mataki da ya zo gabanin fara rabon man a faɗin ƙasa daga 15 ga watan Agusta.

:::Yau 15 ga Nuwamba, jihar Kaduna ke cika shekaru 105 da kafuwa

Shugaban hulɗa da jama’a na matatar, Anthony Chiejina, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa rage farashin ya biyo bayan faɗuwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

A baya-bayan nan, kamfanin man Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin fetur zuwa naira 925 a wasu tashoshinsa dake Legas, daga naira 915.

Dangote ya ce sun sayi motoci 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) don sauƙaƙa rabon mai ba tare da cajin ƙarin kuɗin sufuri ba.

Za su raba mai kai tsaye ga masu gidajen mai da masana’antu da kamfanonin sadarwa da sauran manyan masu amfani da mai.

Kamfanin ya kuma sanar da bada bashin sati biyu ga waɗanda ke sayen lita 500,000 na fetur ko man gas na dizil, inda za a ba su ƙarin lita 500,000 a bashi idan sun cimma sharaɗi.

Dangote ya ce wannan mataki ya yi daidai da manufar tattalin arzikin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

BBCHAUSA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here