Gwamnatin Kano ta umarci al’umma su kare kansu daga yan daba da masu kwacen waya

0
30
Kano

Gwamnatin jihar Kano ta umarci al’umma musamman matasa da yan bijilanti su tashi tsaye su kare kansu daga hare-haren yan daba da masu kwacen waya, wanda suke neman zama wata babbar masifa a kwaryar birni da kewaye.

Kwamishinan tsaron cikin gida, AVM Ibrahim Umar, mai ritaya, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, yayin da ya kai ziyarar jajantawa al’ummar Tudun Fulani da Kurna, akan yadda fadan daba yake janyo asarar dukiyoyi da rayuka, sakamakon kisan wani mutum a yankin.

:::CBN ya takaitawa al’umma adadin kudin da zasu cire daga asusun su na banki a kowanne mako

Yace yanzu ba lokaci ne da matasa da yan bijilanti zasu rika jin tsoro ko gujewa yan daba da masu kwacen waya bane, yana mai cewa dole matasa su kare kansu da iyalan su daga wannan barazana ta kwacen waya da aikin daba.

Kwamishinan ya kara da cewa kamata yayi kowa ya bayar da tasa gudunmawa wajen magance matsalar, ba wai a tsaya ana zagin gwamna a kafar zada zumunta ba, inda yace lokaci ne da za’a yi maganin yan daba in sun kawo farmaki.

Daily News 24, ta rawaito cewa kwamishinan ya umarci matasa su yi maganin yan daba a duk lokacin da suka kawo hari, inda ya nemi a koyawa bata garin hankali kafin yan sanda su zo.

Daga karshe kwamishinan ya yabawa jami’an yan sanda akan yadda suka kama mutanen da suka aikata kisan kai ga wani mutum a yankin Tudun Fulani da Kurna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here