Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin farar hula, lauyoyi, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin addini.
Sanarwar ta ce, “Wannan shiri ya biyo bayan kiran da gwamnatin jihar ta yi tun da farko na gayyatar al’ummomi da su gabatar da buƙatunsu na sabbin masarautun gargajiya.
:::Bashin da ake bin Nigeria ya haura Naira Triliyan 142
Kwamitin yana da alhakin tantance waɗannan bukatun bisa ƙa’idar adalci, daidaito, shigar da kowa cikin harkokin siyasa da zamantakewa, da ɗorewar tattalin arziki.”
Alhaji Hamza Koshe ne zai jagoranci kwamitin, tare da Mai Shari’a Habibu Idris a matsayin Mataimakin Shugaba. Sauran mambobin sun haɗa da manyan jami’an gwamnati, masu ba da shawara na musamman, da wakilai daga Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Ƙungiya Jama’atu Nasril Islam (JNI), Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Kungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), da kuma hukumomin tsaro daban-daban.
Gwamna Bala Mohammed zai ƙaddamar da kwamitin ranar Alhamis, 3 ga Yuli, a Gidan Gwamnatin jihar Bauchi, da karfe 10:00 na safe, in ji Gidado.
Ya ƙara da cewa duk wannan tsari na da nufin ƙarfafa masarautun gargajiya, inganta shigar jama’a cikin harkokin mulki, da kuma raya al’adun jihar.