An sanar da bayan sallar La’asar ta yau Talata a matsayin lokacin gudanar da jana’izar fitaccen attajirin nan Alhaji Aminu Ɗantata a masallacin Madina.
Mustapha Junaid, mataimaki na musamman ga marigayin ya shaida wa BBC cewa shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’izar.
yace an ɗauki marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga filin jirgi na Madina kuma yanzu haka za a je Shakzura inda a nan ne za a ƙarasa shirya shi kafin daga bisani a kai shi haramin Madina domin gudanar da sallah kamar yadda hukumomin Saudiyya suka amince.
:::Hukumomin Saudiyya Sun Amince a Binne Aminu Dantata a Madina
A ranar Asabar ne shahararren ɗankasuwa Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya.
A shekarar Hijira (ta Musulunci) kuma, ya rasu yana da shekara 97.
Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya.