Bashin da ake bin Najeriya yakai Naira triliyan 149.39

0
19
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39, biyo bayan fitowar bayanai daga ofishin kula da bashi na ƙasa, wanda ya nuna cewa an samu ƙaruwar Naira tiriliyan 27.72 a bana idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 121.67 da aka samu a 2024.

An samu ƙarin adadin ne sakamakon faduwar darajar Naira, wanda hakan ke ci gaba da shafar darajar bashin da ƙasar nan ta karbo daga kasashen waje.

:::Bayan sallar La’asar za’a yi jana’izar Dantata a Madina

Dangane da bayanan ofishin DMO, bashin da ake bin Najeriya a waje zuwa ranar 31 ga Maris, ya kai Naira tiriliyan 70.63 kwatankwacin dala biliyan 45.98, wanda ya ƙaru daga Naira tiriliyan 56.02 wato dala biliyan 42.12.

Najeriya ta karbi bashi kama daga kasashen waje da dama da kuma cibiyoyin kudi, ciki har da Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka, sai kuma lamunin bankin Exim na kasar Sin, da kuma wanda ta karba daga Japan da sauransu baya ga bashin kasuwanci na Eurobonds da shima ta karba.

Yawan bashin da kasar ke ciyowa dai na da tasiri sosai wajen sauya farashin kayan masarufi da kuma yanayin tafitar tattalin arzikin kasar da alumma.

RFIHAUSA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here