Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP, sun fara wani babban taron sirri a birnin tarayya Abuja.
An gudanar da wannan taro mai muhimmanci a Otal ɗin Transcorp Hilton, a wani ɓangare na shirin ƙaddamar da wata sabuwar haɗakar jam’iyyu domin fuskantar Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen 2027.
Baya ga Atiku da Lamido, wasu manyan shugabannin PDP da suka halarci taron sun haɗa da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Prince Uche Secondus, da tsoffin gwamnonin jihohi irinsu Aminu Tambuwal (Sokoto), Liyel Imoke (Cross River), Babangida Aliyu (Niger), da Sam Egwu (Ebonyi).
Wata majiya daga wajen taron ta tabbatar da cewa David Mark ne ke jagorantar zaman, kuma ana tattaunawa kan yiwuwar ko shugabannin PDP za su bayar da cikakken haɗin gwiwa ga sabuwar jam’iyyar da ake shirin kafa wa domin zaɓen 2027, ko kuma za su ci gaba da zama a PDP tare da kafa kawancen zaɓe kawai.
Sauran fitattun jiga-jigan PDP da suka halarci taron sun haɗa da Sanata Ben Obi, tsohuwar Shugabar Mata ta PDP ta ƙasa, Josephine Anenih, tsohon Sakataren Tsare-tsare na Jam’iyya, Sanata Austin Akobundu, tsohon Sakataren Yaɗa Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, da tsohon Shugaban Matasa na PDP na ƙasa, Abdullahi Maibasira, da sauransu.