Makusantan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata sun tabbatar da cewa an ɗage gudanar da jana’izarsa da aka tsara gudanarwa bayan sallar La’asar a ranar Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa yanzu an mayar da lokacin jana’izar zuwa bayan sallar Magariba, a cikin haramin birnin Madina.
A wata tattaunawa da Mustapha Junaid, wanda shi ne mataimaki na musamman ga marigayin, ya shaida wa BBC cewa tuni aka kai gawar marigayin zuwa birnin Madina.