Wani mutum mai suna Salisu Musa, ɗan shekara 50, ya rasa ransa bayan faɗawa cikin rijiya a kauyen Gora, na ƙaramar hukumar Madobi ta jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta bayyana cewa ana kyautata zaton Salisu Musa na fama da wata matsalar dake damun sa lokacin da ya fice daga gida ba zato ba tsammani, inda daga baya ya faɗacikin rijiyar.
Duk da ƙoƙarin da jami’ai suka yi domin ceto shi, sun same shi a cikin yanayi na galaba ita, kuma daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa, tare da mika gawarsa ga jami’an ‘yan sanda na Madobi.
A wani lamari dabam kuma, wata mata mai suna Maryam Bita, mai shekara 37, ta tsallake rijiya da baya bayan fādowa cikin wata rijiya da ke kan titin France a ƙaramar hukumar Fagge.
Hukumar kashe gobara ta Kano ta bayyana cewa ta amsa kiran gaggawa cikin hanzari, inda ta samu nasarar ceto Maryam daga cikin rijiyar a raye.
An garzaya da ita asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin samun kulawar likitoci kafin a mika ta ga sashin ‘yan sanda na Sabon Gari.
Hukumar ta bukaci al’umma da su rika sanya ido tare da kare yankunan da ke da rijiya ko wasu hanyoyin ruwa domin gujewa afkuwar irin wannan hatsari.