Wani matashi ya mutu bayan shiga gidan mutane yin fashi da makami a Kano

0
24
Kano

Wani mutum da ake zargi da aikata fashi da makami, mai Musa Nuhu, ya rasu bayan yayi yunkurin aikata fashin a Unguwar Jakada, yankin Dorayi Babba da ke cikin Jihar Kano.

Daily News 24 ta ruwaito cewa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

A cewar SP Kiyawa, wanda ake zargin ya shiga cikin wani gida da ke yankin dauke da wuka, inda ya ji wa mata biyu rauni a lokacin harin.

Ya ce wani namiji da ke cikin gidan ne ya yi ihu tare da tinkarar wanda ake zargin, inda su biyun suka samu raunuka a yayin fafatawar.

An garzaya da wanda ake zargin zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here