Taron PDP ya rikiɗe zuwa tarzoma 

0
26

Taron kwamitin  amintattu na jam’iyyar PDP da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin ya rikide zuwa rikici, bayan jami’an tsaro sun tilasta fitar wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar daga dakin taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC).

An shirya gudanar da taron ne a dakin taron NEC dake hedikwatar jam’iyyar a Abuja, inda mambobi suka fara isa wajen tun da wuri.

Sai dai rikici ya barke yayin da jami’an tsaro suka tilasta fitar wasu mambobi biyu daga dakin taron.

A yayin da ake ƙoƙarin fitar da su da karfi, ƙofar gilashi ta karye, lamarin da ya kara tayar da hankali a wajen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here