Shekaru huɗu kacal zanyi in na zama shugaban ƙasa—Peter Obi

0
26

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ba zai wuce wa’adin shekara huɗu da aka ɗora masa ba.

Obi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka gudanar ta kafar “Twitter Space” ƙarƙashin shirya-shiryen Parallel Facts a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa duk wani ɗan siyasa daga Kudancin Najeriya da ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027, wajibi ne ya kammala wa’adinsa a ranar 28 ga Mayu, 2031, bisa yarjejeniya ta fahimtar juna da ake da ita tsakanin yankin Arewa da Kudu domin zagayawar mulki.

“Ina goyon bayan tsarin rabon mulki da ke bai wa dukkan yankuna damar jagoranci. Idan muka samu tikiti bisa yarjejeniya, zan mutunta ta. Ba zan ƙara rana guda ba fiye da shekara huɗu,” in ji Obi.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ɗin na cikin manyan ’yan siyasa da ake ganin na iya kafa kawance da wasu fitattun jiga-jigan siyasa irinsu Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi, da Nasir el-Rufai, domin ƙoƙarin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here