Matasa 95 Sun Samu Horon Fasahar Kasuwancin Zamani a Jihar Kano

0
20

Akalla matasa 95 a jihar Kano ne suka samu horo a fannin kasuwancin zamani ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar fasaha (AI) da aikace-aikacen zamani wajen samar da abinci, tallace-tallace, da kuma bunkasa darajar kayayyakin gona.

Wannan shiri yana da nufin rage zaman kashe wando a tsakanin matasa, karfafa dogaro da kai, da kuma bunkasa harkar noma a jihar Kano.

Matasa da aka horas an ba su takardar shaidar kammala karatu daga London Academy Business School (LABS), tare da hadin gwiwar Jami’ar Sunderland ta kasar Birtaniya da kuma AA Zaura Foundation International a wani biki da aka gudanar a karshen mako a Kano.

Da yake jawabi yayin bikin, mai kafa AA Zaura Foundation International, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya bayyana cewa, wannan shirin zai ba matasa damar kirkirar damar kasuwanci da kansu maimakon jiran wani ya samar musu.

Ya kara da cewa, shirin yana da burin karfafa gwiwar matasa domin su kafa kasuwancin noma da fasaha (Agri-Tech), su jawo hannun jari, da kuma samar da guraben ayyuka ta hanyar amfani da kayan aikin zamani don sauya fasalin noma da bunkasa yawan amfanin gona.

A nasa jawabin, Daraktan kasa na LABS, Dr. Abdullahi Usman, ya bayyana cewa, yadda kasuwanci ke tafiya a yanzu ya sauya zuwa tsarin dijital, kuma yana da matukar muhimmanci a horas da matasa kan wannan fanni domin su ci moriyar cigaban zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here