Jirgin mahajjatan Kano sahu na 5 ya baro Jidda zuwa Kano
Jirgin sahu na biyar na kan hanyar sa ta dawowa daga ƙasa mai tsarki zuwa Kano.
Jirgin dai na dauke da mahajjata 548, inda ya tashi daga Filin Jirgin Sama na sarki Abdulaziz da ke Jidda zuwa Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mahajjatan da ke cikin jirgin sun fito ne daga kananan hukumomi takwas na jihar.
Daraktan Hukumar Jin DaÉ—in Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Danbappa, ya bayyana jin daÉ—insa kan yadda dawowar mahajjatan ke gudana cikin tsari da kwanciyar hankali, inda ya tabbatar da cewa dukkan mahajjatan na cikin koshin lafiya.
Ya bayyana cewa jirgin mallakin kamfanin Max Air ne ke jigilar mahajjatan daga Jeddah zuwa Kano.