Jami’an tsaro sun hana mambobin Kwamitin Amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP gudanar da taronsu a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.
A safiyar Litinin ne jami’an tsaro suka dakatar da mambobin daga shiga dakin taron Kwamitin Zartaswa na Kasa (NEC), inda suka shirya gudanar da taron.
A karshe dai, taron ya koma zuwa Cibiyar Yar’Adua da ke tsakiyar birnin Abuja.