Gwamnonin Rivers, Plateau, Kano da Bayelsa Za Su Koma APC Cikin Watanni Biyu — Arodiogbu

0
58

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa (Yankin Kudu Maso Gabas), Ijeoma Arodiogbu, ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau da Kano na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki nan da watanni biyu masu zuwa.

A wata hira da jaridar Punch, Arodiogbu ya bayyana cewa wannan shiri ba jita-jita ba ne, kuma ba wani abu ne da za a yi mamaki ba, domin tabbas zai faru nan ba da jimawa ba.

Ya bayyana cewa har ila yau, jam’iyyar APC na bude kofar karɓar Gwamna Peter Mbah na Enugu da Gwamna Alex Otti na Abia idan har suna da sha’awar sauya sheka zuwa jam’iyyar.

“Ina magana ne a bayyane game da gwamnonin Bayelsa, Rivers, Plateau da Kano. A cikin watanni biyu masu zuwa, za ku ga sun shiga jam’iyyarmu a hukumance,” in ji shi.

“Bayelsa na cikin jerin jihohin da za su sauya sheka, shi ya sa na ambace ta. Amma game da Gwamna Adeleke na Osun, ba zan iya tabbatar da komai ba a yanzu — sai dai na san yana kokarin wani abu.”

Arodiogbu ya kuma caccaki ‘yan siyasar adawa da ke kokarin hada kawancen jam’iyyun adawa don tinkarar zaben 2027, yana mai cewa burinsu kawai shi ne su shahara a kafafen yaɗa labarai, ba don ciyar da ƙasa gaba ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here