Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana da niyyar komawa jami’a domin ci gaba da karatu bayan ya yi ritaya daga siyasa.
Ya bayyana haka ne yayin bikin kammala karatu na ɗalibai 205 a makarantar Pacesetters’ Schools da ke Abuja.
Atiku ya ce ilimi shi ne ginshiƙin rayuwarsa, kuma ya fi kowanne zuba jari muhimmanci.
Ya yabawa wanda ya kafa makarantar, Barrister Kenneth Imansuangbon, bisa jajircewarsa wajen inganta ilimi, tare da shawartar makarantar da ta faɗaɗa harkokin ta zuwa matakin jami’a.
Ya kuma bukaci a ƙara saka hannun jari a bangaren ilimi da ƙirƙirar tsarin karatu da zai tallafa wa matasa su zama ’yan kasuwa masu dogaro da kai.