Dakataccen gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa zai iya yin kowace irin sadaukarwa matuƙar hakan zai kai ga zaman lafiya da cigaban jihar.
Fubara ya bayyana haka ne a ranar Asabar a birnin Fatakwal yayin da yake jawabi ga magoya bayansa, inda ya tabbatar da cewa yanzu sun sasanta da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ya ce ya fahimci cewa akwai wasu daga cikin magoya bayansa da ba za su ji daɗin wannan sasanci ba, amma ya roƙe su da su yi haƙuri, domin wani lokaci dole ne a ɗauki matakan da wasu ba za su ji daɗi ba, domin samun mafita mai ɗorewa.
“Duk wanda ya san irin ƙoƙarin da muka yi, ya san cewa babu wani abu da ya fi muhimmanci a gare mu kamar zaman lafiya,” in ji Fubara.
Ya ci gaba da cewa: “Babu wanda zai iya musanta irin gudunmuwar da Ministan Abuja Nyesom Wike ya ba ni. Ko da mun samu saɓani a wasu batutuwa, amma ya taka rawa sosai a wannan tafiya. Don haka ina kira ga duk wanda ke ƙaunata da gaskiya, da ya ajiye son rai, yanzu lokaci ne na neman zaman lafiya.”