Wutar daji ta afkawa tsakiyar Isra’ila

0
15

Wutar daji ta afkawa tsakiyar Isra’ila

Wata gagarumar wutar daji ta tashi a yankin Ness Ziona da ke kusa da birnin Tel Aviv, na Isra’ila lamarin da ya haifar da babbar asara ga wasu gidaje.

 Saboda tsananin gobarar, hukumomin kasar sun dauki matakin gaggawa na kwashe mazauna yankin domin kare rayukansu. 

Gidan rediyon Rundunar Sojin Isra’ila ne ya ruwaito hakan a ranar 26 ga Yunin shekarar 2025.

Ko a kwanakin baya makamanciyar wannan gobara ta afkawa Isra’ila inda ta janyo asara mai yawa.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here