Sojoji sunce sunyi luguden bama bamai akan ƴan ta’addan Jihar Neja

0
44
Sojin sama

Rundunar Sojin Sama ta ƙasa bangaren Operation FANSAN YAMMA, ta kaddamar da luguden wuta a Jihar Neja, wanda ya hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da tallafa wa dakarun ƙasa da ke kai farmaki kan masu alhakin hare-haren baya-bayan nan.

Wannan farmaki ya gudana ne tsakanin ranakun 24 zuwa 26 ga Yuni, 2025, bisa sahihan bayanan leƙen asiri, kamar yadda Daraktan Hulɗa da Jama’a da Bayani na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana a wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a a Abuja.

A cewarsa, ta hanyar haɗin guiwar rundunonin tsaro da hukumomin gwamnati, an gano ayyukan ta’addanci da suka haɗa da hare-hare da satar shanu a ƙauyukan Kakihun da Kumbashi.

Ejodame ya ce rundunar ta Sojin Sama ta gaggauta tura jiragen yaƙi, inda ta aiwatar da jerin hare-hare na musamman da suka hallaka ‘yan ta’adda da dama, suka lalata kayayyakin aikinsu, tare da tarwatsa yunkurin su na sake haɗuwa.

Ejodame, ya ƙara da cewa wannan farmaki ya nuna kwarewar Sojin Sama na Najeriya, da saurin daukar mataki, da kuma haɗin kai mai ƙarfi da dakarun ƙasa da sauran hukumomi ke dashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here