Rundunar Sojin kasar nan ta sanar da fara zaman makoki na kwanaki uku domin girmama sojoji 17 da suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da aka kai musu a Kwana Dutse, karamar hukuma da ke cikin jihar Neja.
Zaman makokin zai gudana daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Yuni, 2025, a matsayin alamar juyayi da girmamawa ga jaruman da suka sadaukar da rayukansu wajen kare martabar ƙasa da tsaron al’umma.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, rundunar ta umarci dukkan cibiyoyi da ma’aikatan soji a faɗin ƙasa da su sauke tutar Soji zuwa ƙasa-ƙasa a tsawon lokacin makokin.
Rundunar ta bayyana wannan mataki a matsayin shaida cewa tana daraja rayuwar jami’anta, tare da nuna alhini da jajantawa ga iyalai da ‘yan uwa na waɗanda suka rasa rayukansu.
An tabbatar da mutuwar sojojin ne sakamakon hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai kan sansanonin soji da ke jihohin Neja da Kaduna.