Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa an samu zaman lafiya a Jihar Rivers.
Wike ya bayyana cewa shi da Gwamnan da aka dakatar na jihar, Siminalayi Fubara, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar sun sasanta rigimar dake tsakanin su.
Ya bayyana haka ne bayan wani taro da aka gudanar a daren jiya a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, inda aka hadu da dukkan ɓangarorin da rikicin ya shafa.
Tun da dadewa Wike da Fubara suna cikin rikici dangane da mulkin Jihar Rivers, wanda rikicin ya bazu har ya shiga Majalisar Dokoki ta Jihar.
Rikicin ya kai ga ɗaukar matakai na shari’a da dama, inda Kotun Koli ta yanke hukunci a goyon bayan ‘yan majalisar.
Sai dai wannan hukunci ya haifar da wani sabon rikici, inda ‘yan majalisar tare da Wike suka fara barazanar tsige gwamnan.
A watan Maris, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Rivers bayan da rikicin ya fara barazana ga zaman lafiya. Wannan matakin ya haɗa da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukan ‘yan majalisar dokokin da aka zaɓa.
Shugaban ƙasa ya kuma naɗa Tsohon Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas, a matsayin mai kula da mulkin jihar na wucin gadi.
Amma a yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron, Wike ya bayyana cewa zaman lafiya ya dawo cikin jihar.
Ya ce, mun amince gaba ɗaya da mu yi aiki tare da gwamna, kuma gwamnan ma ya amince da yin aiki tare da mu.