Kamfanin NNPC yayi zarcen cewa ana shirya masa maƙarƙashiya 

0
26

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPC, ya zargi wasu mutane tare da wasu daga cikin ma’aikatansa da kaddamar da wata haɗaɗɗiyar makarkashiya don bata sunan shugabancin kamfanin da kuma hana ci gaban sauye-sauyen da ake aiwatarwa a halin yanzu.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, 27 ga Yuni, 2025, NNPC ya bayyana wannan yunkuri a matsayin kokarin aiwatar da ɓarna da gangan da nufin yaɗa ƙarya da bayanan bogi don karkatar da hankalin jama’a da kuma hana shugabancin kamfanin mayar da hankali kan muhimman gyare-gyare.

Kamfanin ya ce waɗanda ke bayan wannan yunkuri sun haɗa da wasu da aka sani da kuma wasu da ba a san su ba waɗanda ke jin tsoron jajircewar kamfanin wajen bin gaskiya.

“Wannan wani shiri ne da aka tsara domin hana ci gaban sauye-sauyen gaskiya, da shugabanci na gari, da sauya kamfani zuwa wanda ke aiki bisa doka da ƙa’ida,” in ji sanarwar. 

Wannan alama ce ta yadda wasu ke shirin yin duk mai yiwuwa don dakile sauya fasalin kamfanin man fetur na ƙasa.

NNPC, ya zargi ƙungiyar da ke da hannu a wannan yunkuri da yaɗa labaran ƙarya da masu tayar da hankali da nufin hana ci gaba da rage kwarin gwiwar ma’aikatan da ke marawa sauyi baya.

Duk da wadannan ƙalubale, NNPC ya sake jaddada cewa zai ci gaba da mai da hankali kan aikinsa na sauya kamfanin zuwa cikakken mai aiki da gaskiya da hangen nesa.

“Za mu iya fuskantar ƙarin yaɗa jita-jita da ƙage nan gaba, amma hakan ba zai dakile mu ba,” in ji kamfanin. “Muna kira ga ma’aikatanmu, masu ruwa da tsaki da dukkan ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su ci gaba da daurewa, su kau da kai daga hayaniya. Sauyi yana kan tafiya, kuma ba wanda zai dakile shi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here