Zan yi duk abin da Tinubu ya buƙata a zaɓen 2027—Barau

0
34
Jibrin-Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya bayyana cewa zai yi duk abin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙata daga gare shi a shekarar 2027.

Barau ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Laraba, a gabanin jin ra’ayin jama’a da kwamitin majalisar dattawa kan sauya kundin tsarin mulki zai fara gudanarwa a jihohin ƙasa.

Da yake amsa tambayoyi dangane da kiraye-kirayen da ake yi masa da ya kasance ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa tare da Tinubu a zaɓe mai zuwa, Barau ya ce lokaci bai yi ba da za a fara magana kan siyasar 2027.

“Gaskiya, bana son in ce komai a yanzu. Abin da ya ke a bayyane shi ne, tun daga farkon wannan gwamnatin, Shugaba Tinubu yana aiki tukuru domin canza alkiblar wannan ƙasa,” in ji shi.

Barau ya ce Tinubu ya gaji ƙalubale masu tarin yawa, amma yana da jajircewa wajen inganta cigaban ƙasa.

“Muna aiki tare da shi dare da rana saboda shi uba ne ga ƙasa. A wannan lokaci, ba ma buƙatar tattaunawa kan batun ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, aikin da ya ke yi yana kan hanya, kuma dole mu goyi bayan sa gaba ɗaya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ya kamata kungiyoyin da ke mara masa baya su mayar da hankali kan kyautata mulki da cigaban ƙasa a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here