Waiya ya taya sabbin shugabannin kungiyar wakilan kafafen yada labarai murnar rantsar dasu

0
19

kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar kano, kwamared ibrahim abdullahi waiya, ya taya sabbin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta najeriya (nuj), reshen wakilan kafafen yaɗa labarai murnar rantsar da su, a madadin gwamnatin jihar kano.

sanarwar hakan na cikin wata sanarwar da daraktan harkokin musamman na

ma’aikatar yada labarai da harkokin cikin gida ta jihar kano, sani abba yola, ya fitar a yau alhamis.

 sabbin shugabannin dai sun kasance karkashin jagorancin kwamared murtala adewale, a matsayin shugaba.

kwamishinan ya bayyana cewa, zabinku cikin kwanciyar hankali da tsarin dimokuraɗiyya alama ce ta yarda da amincewar da abokan aikinku ke da ita game da nagartar ku wajen jagoranci da gaskiya, hangen nesa da kuma kishin aiki.

 ina kuma yaba wa shugabannin da suka sauka bisa jajircewarsu da gudunmawar da suka bayar, wanda ya gina tushe mai ƙarfi don ci gaba da haɓaka aikin jarida cikin ƙwarewa da kishin gaskiya, inji shi.

kwamared waiya ya jaddada muhimmancin rawar da ‘yan jarida ke takawa musamman mambobin wakilan kafafen yada labarai, wajen tsara muhawarar jama’a da kuma yada manufofin gwamnati.

ya kwatanta correspondents’ chapel da madubi da duniya ke kallon ci gaban da ake samu a jihar kano ta hannunsu, tare da ƙarfafa gwiwar mambobin da su ci gaba da tsayawa kan gaskiya, daidaito da adalci wajen bayar da rahotanni musamman a wannan lokaci da ake fuskantar kalubalen yaɗuwar labaran ƙarya.

daga ƙarshe, kwamishina waiya ya yi fatan alheri da nasara ga sabbin shugabannin a sabuwar aikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here