Babban jami’in ɗan sanda ya kashe kansa a jihar Neja

0
15

Wani sufeton ƴan sanda mai suna Bassey Asuquo ya kashe kansa a garin Sarkin-Pawa, na karamar hukumar Munya da ke Jihar Neja.

Rahoton da shafin Zagazola Makama, wanda ke kawo labarai kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ya kawo ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:59 na daren ranar Laraba.

Asuquo, jami’i ne a rundunar ƴan sandan tafi-da-gidanka ta 28 (PMF) da ke Umuahia, Jihar Abia, wanda aka tura zuwa yankin Neja domin gudanar da wani aiki na musamman.

Rahoton ya bayyana cewa tun bayan zuwansa wannan aikin, an fara lura da canje-canje na halayya a tare da shi, lamarin da ya sanya kwamandan rundunar ya umurci a karɓe bindigar aikin da ke hannunsa tare da ajiye ta a ofishin ƴan sanda na Sarkin-Pawa.

Sai dai, duk da an karɓe bindigar sa, rahotanni sun ce Asuquo ya yi amfani da bindigar wani abokin aikinsa wanda ke cikin barci, inda ya harbe kansa har lahira.

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda mai magana da yawunta a Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce tuni aka fara gudanar da bincike kan musabbabin lamarin.

Zuwa yanzu an kai gawar mamacin zuwa dakin ajiye gawa mafi kusa da inda lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here