Ƴan sandan Kano sun kwato babur mai kafa uku guda 6 daga wajen ɓarayi

0
29

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta samu nasarar bankado wata kungiyar masu sace babura kirar masu kafa uku inda ta kama mutane hudu da ake zargi da hannu a aikata laifin, ciki har da mace guda. 

Wannan na zuwa ne bayan samun sahihan bayanai daga wasu da ke da masaniya kan aikata sace baburan.

Sanarwar da rundunar ta fitar a yau Alhamis tace, ranar 17 ga Yuni, 2025, jami’an ‘yan sanda sun kama Auwal Mohammed, mai shekara 30 daga unguwar Hotoro, a Kano da Maryam Ibrahim, mace ‘yar shekara 25 daga Jihar Bauchi, a karamar hukumar Kura ta jihar Kano, kan zargin su da kokarin kwace babur ɗin wani  Shu’aibu Aliyu.

Saurin daukar matakin da ‘yan sanda suka yi ya taimaka wajen kubutar da babur din daga satar. Bayan zurfafa bincike, an gano cewa wasu mutane biyu na karɓar baburan da ake sacewa wato Suleiman Lawal wanda aka fi sani da Aljan, ɗan shekara 25 daga unguwar Sheka da kuma Muhammad Tajuddeen, ɗan shekara 32 daga Kundila Quarters suna da hannu a wannan aika-aikar, inji rundunar.

 Rundunar ta ce ta kama su duka kuma an kwato jimillar babura guda shida da aka sace daga hannunsu.

Rundunar ta jaddada cewa za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu domin su fuskanci hukuncin doka bisa yadda bincike zai tabbatar da laifinsu.

Haka kuma, rundunar ta shawarci jama’a da su kasance masu kula da tsaro da kuma fahimtar dabaru da irin wadannan bata-gari ke amfani da su.

Daga ƙarshe, duk wanda aka sace masa Keke Napep na baya-bayan nan, an bukace shi da ya tuntubi hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai, ofishin jami’in hulɗa da jama’a (PPRO), ko kuma ya kira lambar 07014601313 domin tantancewa da karɓar babur dinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here