Ƴan bindiga sun kwace ikon ƙaramar hukuma a Katsina

0
30

Rahotanni daga jihar Katsina na nuna cewa wasu ‘yan bindiga masu dauke da makamai, karkashin jagorancin wani shahararren ɗan ta’adda da aka fi sani da Babaro, sun karbe ragamar mulki a karamar hukumar Kankara.

Wani masani a fannin tsaro mai suna Bakatsine ne ya bayyana hakan ta shafinsa na X, inda ya bayyana cewa maharan sun kashe mutane da dama a yankin, tare da hana ayyukan noma da kasuwanci gaba ɗaya. 

Bakatsine yace, noma ya tsaya daga Marabar Kankara zuwa ‘Yantumaki, mutane da dama an kashe su, wasu an yi garkuwa da su, ayyukan kiwon lafiya sun durkushe. Mazauna yankin na rokon Gwamna Dikko Radda da gwamnatin tarayya su kawo musu agaji cikin gaggawa, inji sanarwar.

 Jaridar Leadership, ta ruwaito cewa, karamar hukumar Kankara na cigaba da kasancewa wuri mai cike da barazana, inda ake ci gaba da kai hare-hare.

 A shekarar 2020, an sace dalibai fiye da 300 daga wata makaranta a yankin, wanda hakan ya girgiza kasa baki ɗaya.

Kawo yanzu, gwamnatin jihar Katsina da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan lamari ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here