Zan fice daga APC in har Tinubu ya gaza gyara Najeriya—Ndume

0
18

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu a majalisar dattawa, ya bayyana cewa zai iya ficewa daga jam’iyyar APC idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza gyara Najeriya.

A wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na Arise Television, Ndume wanda ya sha suka kan salon mulkin shugaban kasa a ‘yan kwanakin baya ya bayyana cewa ya halarci taruka da dama na shugabannin jam’iyyun adawa da ke neman haɗa ƙarfi da ƙarfi domin kifar da Tinubu a zaɓen 2027.

Sai dai ya ce har yanzu yana da yakinin cewa Tinubu na iya gyara Najeriya, dalilin da ya sa bai riga ya shiga cikin wannan kawancen ba.

“Ina da masaniya game da wannan kawancen jam’iyyun adawa. Na halarci wasu daga cikin tarukansu. Amma har yanzu ina da imani cewa wannan shugaban zai iya gyara abubuwa. Idan ya gaza, watakila zan bar jam’iyyar. Jirgin da aka ɗora masa nauyi fiye da kima zai nutse,” in ji Ndume.

“Sun sha kira na, amma na sha gaya musu cewa ba zan fito daga wutar tukunya in fada cikin wutar girki ba. Dole ne na tabbatar da inda nake dosa, inji Sanatan

“Ina da imani cewa Tinubu na iya zama shugaban ƙasa mai nasara, wannan shi ne abin da nake fata tun farko. Amma idan ya ci gaba da tafiya haka, ko da kuwa an ɗora wasu gwamnoni ko mutane a cikin wannan jirgi, abin da ake yi shi ne haɗa APC da hatsarin nitsewa,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here