Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ce gwamnatin sa na nazarin dokokin ƙara tsaurara hukunci kan masu bai wa ‘yan ta’adda bayanan sirri, ciki har da hukuncin kisa ko ɗaurin rai da rai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai kauyen Tadurga a ƙaramar hukumar Zuru da kuma Kyebu a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, inda ya bayyana masu bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’adda a matsayin “barazana babba” ga al’umma, yana mai shan alwashin ɗaukar matakin doka mai tsauri a kansu.
Harin da aka kai kwanan nan a waɗannan yankuna biyu ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da raunata wasu da dama, tare da sace dabbobi.
Gwamna Idris ya yi addu’ar neman gafara ga waɗanda suka rasa rayukansu a harin, kuma ya sanar da kammala shirye-shiryen kafa sansanin soja a masarautar Zuru domin ƙarfafa tsaro.
Ya kuma bayyana cewa an samu nasarar samo motocin yaƙi masu sulke da sauran kayan aiki daga Abuja, tare da bayar da umarnin gaggawa don samar da matsuguni na wucin gadi ga dakarun soja kafin a kammala ginin sansani na dindindin.
Gwamnan ya ja kunnen sarakunan gargajiya da al’umma gaba ɗaya da su guji siyasantar da batun tsaro ko wallafa kalaman da ba su dace ba a kafafen sada zumunta.