PDP ta tabbatar da na hannun daman Wike a matsayin sakataren ta na ƙasa
Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa, PDP ta tabbatar da na hannun daman Nyesom Wike, Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren ta na ƙasa.
Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Ambasada Iliya Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar PDP da ke Abuja, a ranar Laraba.
Damagum, wanda Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da sauran jiga-jigan jam’iyyar suka rufawa baya, ya ce matakin amincewa da dawo da Anyanwu cikin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) “mataki ne mai wuya”.
Haka kuma, Damagum ya bayyana cewa an soke zaman taron NEC da aka shirya gudanarwa.
A cewarsa, zamu gudanar da babban taron a nan gaba kaɗan, inda a wannan taron ne za mu yanke shawarar da za ta kai ga gudanar da sahihin taron kwamitin zartarwa.