Hisbah ta hana DJ da Ƙauyawa day, a wani yankin jihar Katsina

0
30

Hukumar Hisbah ta karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina ta sanar da haramta gudanar da taron DJ da wasu bukukuwa irin su Kauyawa Day da Shan Shayi, bisa zargin cewa su na haddasa lalacewar tarbiyya da kuma kara yaduwar amfani da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa.

Sanarwar hakan ta fito a ranar Talata, 24 ga Yuni, 2025, bayan wani taron hadin gwiwa da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Rimi, inda aka tattauna matakan da za a dauka don dakile irin wadannan taruka.

A cewar sanarwar, wannan mataki ya biyo bayan koke-koken da al’umma suka dinga yi dangane da yadda taron DJ da sauran bukukuwa ke zama wata kafa ta yada fasadi, barna, da kuma amfani da miyagun kwayoyi, musamman tsakanin matasa.

Taron ya samu halartar shugaban karamar hukumar Rimi, Hon. Muhammad Ali Rimi, wanda ya jagoranci kafa kwamitin Hisbah na musamman domin hada kai da hukumar ta jiha wajen shawo kan wannan matsala.

Haka kuma, shugaban majalisar kansiloli na karamar hukumar, Hon. Abdullahi Haruna Eka, kwamandan Hisbah na Rimi, Malam Tanimu Abdu, da kuma wakilai daga hukumomin tsaro irinsu ‘yan sanda, DSS, Civil Defence, da shugabannin gargajiya da na addini daga bangarorin Izala da Dariqa duk sun halarci taron.

Hukumar Hisbah ta kuma ja kunnen duk wani da ke gudanar da DJ ko shirya irin wadannan bukukuwa a yankin da ya dakatar da su, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana ci gaba da wannan aiki, zai fuskanci hukunci daidai da doka ba tare da nuna rangwame ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here