Harin ƴan bindiga ya kashe sojoji da dama a jihar Neja

0
7
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rahotonni sun bayyana  cewa sojojin ƙasar nan15 ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka kai musu a wani wuri da ke daf da iyakar jihar Kebbi da kuma Neja a tsakiyar ranar Talata.

Tuni aka kwashe gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka zuwa yankin Mariga na jihar Neja inda sansaninsu yake.

Wasu mazauna yankin Danko Wasagu, sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin karfe 12 na Talata, yayin da yan ta’addan suka kaiwa sojojin hari a yayin da suke tafe a cikin wata babbar mota.

Shugaban ƙaramar hukumar Mariga Abbas Adamu, ya tabbatar da harin tare da kisan sojojin yayin da yake zantawa da RFI Hausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here