Gwamnatin Kano ta bayar da hutun sabuwar shekarar Muslinci
Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, a matsayin ranar hutu domin bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1447 bayan Hijira.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Musulmi murnar ganin sabuwar shekarar, wadda ke farawa da watan Muharram, wata na farko a kalandar Musulunci.
Gwamnan ya bukaci al’ummar Kano da dukkan Musulmai da su yi bitar halayensu da ayyukansu na shekarar da ta gabata, tare da amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban jihar Kano da kasa baki ɗaya.
Haka kuma, Gwamna Abba ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta rayuwar al’ummar Kano ta hanyar gudanar da mulki na gaskiya da ya dogara da bukatun jama’a.