Fitaccen ɗan bindiga Bello Turji, ya kashe fiye da ’yan sa-kai 40 a wani hari da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadin data gabata.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa cikin waɗanda suka rasa rayukansu har da jami’ai huɗu na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da kuma wani tsohon dan bindiga da ya tuba, mai suna Bashar Maniya, wanda ke taimakawa jami’an tsaro da bayanai.
Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya faru a kusa da kauyen Rugar Chida, inda mahaifin Bello Turji ke rike da sarautar gargajiya.
An ce maharan sun yi wa tawagar jami’an tsaro da ’yan sa-kai kwanton-bauna a wani yankin da babu sabis na waya na tsawon makonni biyu, sakamakon wani aikin da sojoji ke gudanarwa a yankin.
A wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, an ga Bello Turji yana murnar nasarar tare da nuna gawarwakin waɗanda aka kashe, ciki har da Bashar Maniya, yana rera wakokin nasara.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa abu ne mai matuƙar takaici da za a iya kauce masa idan akwai hadin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma.
Rahotanni sun bayyana cewa kafin wannan harin, an kashe fiye da ’yan bindiga 30 daga cikin yaran Turji a wata arangama da suka yi da mutanen Bashar Maniya.