Babban Hafsan tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa yunwa da talauci sun zama babbar barazana ga tsaron ƙasa gaba ɗaya.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a yayin bude taron bitar tsaro na ƙasa karo na 14 da Ƙungiyar Tsoffin Daliban Kwalejin Tsaro ta Ƙasa (AANDEC) ta shirya a ranar Litinin a birnin Abuja.
Taken taron shine: “Yadda Za a Yaƙi Yunwa da Talauci Domin Samar da Zaman Lafiya da Cigaba mai Dorewa a Najeriya.” Taron ya gudana ne tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro.
A cikin jawabin da Kwamandan Horar da Sojojin Ƙasa, Rear Admiral Ibrahim Shettima ya karanta a madadin sa, Janar Musa ya jaddada cewa akwai bukatar haɗin gwiwar dukkan sassan ƙasa don tunkarar matsalolin yunwa da talauci, yana mai bayyana yadda hakan ke da nasaba da tsaro a cikin gida.
Ya bayyana godiya ga masu shirya taron, inda ya ce wannan dandali wata muhimmiyar dama ce ta tattauna hanyoyin da za a bi wajen magance ƙalubalen tsaro da kuma inganta cigaban ƙasa.