Jam’iyyar SDP ta dakatar da shugaban ta na ƙasa

0
17

Jam’iyyar SDP ta dakatar da shugaban ta na ƙasa

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar SDP ya dakatar da Shugaban ta na Ƙasa Alhaji Shehu Gabam, tare da wasu mambobin kwamitin guda biyu, wato Nze Nnadi Clarkson, mai duba harkokin kuɗi na jam’iyyar, da Uchechukwu Ogbonna Chukwuma, Shugaban Matasa na Ƙasa, bisa zargin aikata manyan laifukan da suka shafi kudaden jam’iyyar, satar kuɗi, da karkatar da dukiyoyin jam’iyya.

Wannan dakatarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar.

A cewar sanarwar wannan matakin ya biyo bayan wani zama da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa suka yi, inda aka gabatar da kwararan hujjoji da ke haɗa waɗanda aka dakatar da aikata mu’amalar kuɗi ba tare da izini ba, da shirye-shiryen ƙara wa kansu arziki, da kuma cire kuɗaɗen jam’iyya daga asusun banki ba tare da amincewar kwamitin gudanarwa ba.

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa wannan lamari ya fara bayyana ne bayan da aka gano cewa Shugaban jam’iyyar ya tura wani bayanin kudi ga Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC) ba tare da izini ba. 

A cewarsa, an yanke wannan hukunci ne domin bai wa hukumomin da abin ya shafa damar gudanar da cikakken bincike. “Dole ne jam’iyyarmu ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya da rikon amana,” in ji shi.

Jam’iyyar ta kafa wani kwamitin bincike na wucin gadi domin duba takardun kuɗi da duba yiwuwar ɗaukar ƙarin matakan ladabtarwa ko na doka.

A halin yanzu, Mataimakin Shugaban Ƙasa daga Arewa, Dr. Sadiq Umar Abubakar, ya karɓi ragamar jagorancin jam’iyyar a matsayin Shugaban riko, kamar yadda kundin tsarin mulki na jam’iyyar ya tanada.

Aiyenigba ya bayyana cewa kuɗaɗen da ake zargin an karkatar sun kai daruruwan miliyoyin naira, ciki har da gudummawa da kudaden da aka samu daga siyar da fom ɗin tsayawa takara a zaɓen 2023, da sauran kuɗaɗe daga asusun jam’iyya.

Sanarwar ta ƙara da cewa an riga an sanar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da sauran hukumomin da abin ya shafa game da dakatarwar.

A ƙarshe, ya jaddada cewa dakatarwar Alhaji Shehu Musa Gabam, Nze Nnadi Clarkson, da Uchechukwu Ogbonna Chukwuma ta fara aiki nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here