Iyalan mafarauta 16 ƴan Kano da aka kashe a Edo sun ce gwamnati bata biya su diyyar da tayi alƙawari ba

0
12

Iyalan mafarauta 16 ‘yan asalin Jihar Kano da aka kashe a garin Uromi da ke Jihar Edo, sun bayyana cewa har yanzu gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta ɗauka na tallafa musu da biyan diyya.

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga harin, tare da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, sun ce alkawuran da gwamnoni da hukumomin Jihohin Kano da Edo suka yi na biyan kuɗin magani, tallafi da diyya sun tsaya ne kawai a fatar baki, amma ba a aiwatar da komai ba.

Mafarautan, waɗanda suka fito daga yankin Toronkawa a Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano, da kuma wasu abokansu daga ƙananan hukumomin Garko, Kibiya, da Rano, sun taho ne daga Fatakwal ta Jihar Ribas a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, inda sukagamu da ajalinsu a hannun wasu ’yan banga a Uromi a ranar 28 ga Maris.

’Yan sanda sun tabbatar da kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, sannan gwamnatocin Kano da Edo suka yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace don tallafawa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma gurfanar da masu laifi.

A watan Afrilu, Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya sanar da kafa kwamitin bincike tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya. Wannan ya biyo bayan ziyarar da mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya kai jihar Edo tare da wasu jami’an gwamnati.

Daga baya, Gwamna Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziyya Kano, inda ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma mutanen da suka jikkata a harin.

Shi ma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana a yayin ziyarar Gwamnan Edo zuwa garin Toronkawa cewa gwamnatin Kano za ta yi duk mai yiwuwa don ganin iyalan wadanda abin ya shafa sun samu diyya da tallafi na kayan abinci da kuɗaɗe.

Duk da waɗannan alƙawura, har yanzu ba a ga wani mataki na zahiri daga gwamnati ba. 

Koda aka tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya wanda shi ma mamba ne a kwamitin binciken ya ƙi cewa komai.

Haka zalika, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Edo, Paul Ohonbamu da Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan jihar, Free Itua, ba su amsa kiran waya ko sakonnin da aka tura musu ba.

A nasa bangaren, shugaban al’ummar Hausawa a Edo, Alhaji Badamasi Saleh, ya ce ba shi da wata masaniya game da ko an cika alkawarin da aka yi wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa ko al’adun haka.

Daga bangaren ɗaukar mataki akan waɗanda suka yi kisan ma babu wani ƙarin bayani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here