Babu yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mu da Isra’ila—Iran

0
32

Isra’ila ta sanar da tsagaita wuta a yaƙin ta da Iran

Ministan Tsare-Tsare na Isra’ila, Ron Dermer, ya bayyana wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, cewa gwamnatin Isra’ila ta amince da tsagaita wuta da Iran. 

Wannan bayani ya fito ne daga rahotannin wasu kafofin yada labarai na Isra’ila.

Tunda farko shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da tsagaita wutar, amma Ministan Harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce “kawo yanzu, babu wata yarjejeniyar tsagaita wuta” tsakanin Iran da Isra’ila, yana mai karawa da cewa gwamnatin Tehran za ta daina kai hare-haren ramuwar gayya ne kawai idan Tel Aviv ta daina “kai hare-hare” kan Iraniyawa.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here