Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) na fuskantar zargi kan sakacin da ya haifar da rasuwar wata mai ciki.
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) yana fuskantar zargin sakaci daga iyalan wata mai juna biyu, mai suna Amina Muhammad, wadda ta rasu a asibitin a ranar Lahadin data gabata.
A cewar iyalan, Amina ta rasu ne sakamakon matsalolin da suka taso bayan tiyatar cire juna biyun da take ɗauke dashi wato (CS), wanda suka danganta da sakaci, rashin kwarewa daga ma’aikata, da kuma rashin isassun kayayyakin aiki a dakin tiyata na asibitin.
Wata babbar ‘yar uwarta (wanda ba a bayyana sunanta ba) ta shaida cewa an jinkirta yin CS din saboda bukatar samun jinin da za a iya amfani da shi idan bukatar jinin ta taso, inda tace bayan tiyatar, lafiyar Amina ta kara tabarbarewa har ta kai ga rasuwa.
“Ta shigo asibitin da kanta a ranar Juma’ar da ta gabata, amma an jinkirta kula da ita saboda batun samun jini. Asibiti irin na AKTH ya kamata ya kasance da babban wajen adana jini na zamani,” in ji ‘yar uwar.
“Bayan wannan jinkiri, an yi mata tiyatar ba tare da an saka mata jinin ba, wanda daga nan sai ta fara fama da matsanancin numfashi.
An dora ta kan na’urar taimakawa numfashi ta oxygen amma babu wutar lantarki da za ta kunna na’urar.
Yar uwar mamaciyar tace ma’aikata sun nuna halin ko in kula, rashin kwarewa da kuma rashin tausayi akan Amina
Haka zalika tace sun roki a mayar da ita dakin bayar da kulawar gaggawa (ICU) domin a kula da ita yadda ya kamata, amma suka ki amincewa da haka, tare da mayar da ita dakin haihuwa.
Da aka tuntubi Jami’ar Hulda da Jama’a ta asibitin, Hajiya Hauwa Inuwa Dutse, ta bayyana cewa ta mika bayanan marigayiyar ga hukumar gudanarwar asibitin domin su gudanar da bincike.
“Na riga na mika bayanan marigayiyar ga hukumar gudanarwa. Za su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya da kuma wanda ya yi kuskure. Za mu sanar da jama’a sakamakon binciken da zarar an kammala,” in ji ta.