Ƴan sanda basa taimakawa a murɗe zaɓe a Najeriya—Egbetokun

0
20

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan ƙasa Kayode Egbetokun, ya karyata zargin cewa hukumomin tsaro na da hannu wajen sauya sakamakon zaɓe a Najeriya, yana mai cewa irin waɗannan zargin ba su da tushe kuma ba su da adalci.

Yayin da yake jawabi a taron manyan masu ruwa da tsaki kan dimokuraɗiyya karo na uku da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, Egbetokun ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ba ta da wata alaka da tasiri ko rinjayar da sakamakon zaɓe, domin aikinta ya tsaya ne kan kula da tsaro da tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓe.

Egbetokun, wanda Kwamishinan ‘Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya (FCT), Adewale Ajao, ya wakilta, ya jaddada cewa rawar da jami’an ‘yan sanda ke takawa a lokacin zaɓe ita ce bayar da tsaro da tabbatar da doka, ba wai shishshigi cikin lissafin ƙuri’u ba.

“Ina so in jaddada cewa zargin cewa ‘yan sanda na da hannu a murɗe zaɓe ba komai ba ne face tunanin banza. Ba mu da wani alaƙa da jam’iyyu ko hukumar zaɓe. Ba mu muke  ƙidaya ƙuri’u ba, aikinmu kawai shi ne saka idanu yayin da INEC ke tattara sakamako,” in ji shi.

Wannan jawabi ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce dangane da zaɓen 2023, inda jam’iyyar hamayya ta PDP da ma jam’iyyar mai mulki APC ke zargin juna da hannu a cikin maguɗin zaɓe da wasu gurɓatattun masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here