Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad el-Rufai, ya bayyana cewa ba ƙaramin abu ne zai sanya Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake samun nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027 ba.
A wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, El-Rufa’i ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi nazari a kan yadda rayuwarsu ta kasance tun bayan rantsar da Shugaba Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023 zuwa yanzu.
Ya ce dole ne mu tambayi jama’a su yanke hukunci, idan suna jin daɗin abubuwan da ke faruwa yanzu.
Yana mai cewa wannan sabuwar gwamnati shekara biyu kacal ta yi, idan rayuwar ƴan Najeriya ta inganta tun da aka rantsar da Tinubu, to madalla, amma idan ba haka ba, me ya hana a bawa wasu dama.
El-Rufai ya bayyana cewa binciken jin ra’ayi da ƙungiyarsu ta gudanar a sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman kudu maso gabas da arewa ya nuna cewa kashi 91 cikin ɗari na jama’a ba sa goyon bayan Tinubu ya sake zama shugaban ƙasa.
Ya kara da cewa ko a Jihar Lagos da ke matsayin jiharsa ta haihuwa, adadin rashin goyon bayan da ake yi masa ya kai kashi 78 cikin ɗari.
El-Rufai ya siffanta gwamnatin Tinubu da “gwamnati mai rauni”, yana mai jaddada lalacewar tattalin arziki, rugujewar tsarin tsaro da kuma rashin tabbataccen tsarin kasuwanci da zuba jari.
Tsohon ministan ya kuma nuna damuwa kan rashin gaskiya a harkokin kuɗin gwamnati, inda ya ce duk da karuwar kudaden shiga da gwamnati ke samu, babu wani ci gaba da ake gani a kasa.