Aƙalla fasinjoji 13, ciki har da direban wata mota ta kamfanin Benue Links, sun shiga hannun ‘yan bindiga ta hanyar yin garkuwa dasu a yankin karamar hukumar Okpokwu da ke jihar Benue.
Lamarin ya faru da yammacin ranar Lahadi a kauyen Eke-Elengbecho, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka tare motar da ake zargin na kan hanyarta daga Abeokuta, zuwa birnin Makurdi.
Wata majiya ta bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin ya samu nasarar tserewa, inda ya sanar da jami’an ‘yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Eke.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benue, Udeme Edet, ya tabbatar da faruwar lamarin ga TheCable a ranar Litinin.
“Eh, an dakatar da wata mota, kuma akalla mutane 13, ciki har da direbanta, aka sace,” in ji Edet.