Umarnin INEC ba zai hana mu gudanar da taron kwamitin zartarwa ba—PDP

0
18

Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa, PDP ta bayyana cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ba ta da hurumin hana taron Babban Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NEC) da jam’iyyar ke shirin gudanarwa.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Abuja a ranar Lahadi, Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce shirye-shiryen taron NEC suna tafiya daidai kamar yadda aka tsara.

A baya-bayan nan, INEC ta aike da wasiƙa zuwa ga PDP tana nuna rashin amincewa da yadda aka aiko mata da sanarwar babban taron PDP, bisa hujjar cewa ba Shugaban jam’iyyar da Sakatare na Ƙasa ne suka sa hannu a wasikar ba.

Sai dai Ologunagba ya bayyana cewa Sakataren riƙo na INEC, Halilu Aminu, wanda ya sa hannu a kan wasiƙar, yana ƙoƙarin taimaka wa jam’iyyar APC wajen mayar da  ƙasar nan mai bin tsarin mulkin jam’iyyar siyasa guda ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here